<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>299</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu ne ya yiwo gafara
 Domin masu zunubi.
 Yesu ne ya ba mu sabon rai,
 Rai fa na har abada.

[V2]
 KORUS
 Akwai murna fa da hutu
 Cikin sunan Yesu Mai Ceto
 Domin kullum ya ke nan tare da mu.
 Ba zai bar mu ba, ko kaɗan.

[V3]
 2) Ga alkawaransa wurinmu,
 Za ya cika dukansu.
 Ba zai tashi ko ya bar mu ba
 Har iyakar zamani.
 Korus

[V4]
 3) Za ya biya duk bukatarmu
 Domin zaman duniya
 Bisa ga wadatar Allahnmu
 Cikin Sama, gidansa.
 Korus

[V5]
 4) Kome dai da Za mu yi roƙo
 Cikin sunan Ɗan Allah,
 Allah dai zai cika mana shi
 In mun ba da gaskiya.
 Korus

[V6]
 5) Sai mu riƙa ba da gaskiya,
 Sai mu kau da shakka duk,
 Gama Yesu mai aminci ne,
 Faɗarsa ta tabbata
 Korus</lyrics>
<title>Yesu Ne Ya Yiwo Gafara LW299</title>
</song>